Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Cin Hanci Da Rashawa Ba Ta Sauya Ba A Najeriya - Rahoto


Shugaban Kungiyar CISLAC, Awwal Ibrahim Musa Rafsanjani
Shugaban Kungiyar CISLAC, Awwal Ibrahim Musa Rafsanjani

Najeriya na matsayin na 154 daga cikin jerin kasashe 180 da rahoton ya duba.

Wani rahoto da Kungiyar Yaki da cin hanci da rashawa ta Transparency International tare da kungiyar CISLAC suka fitar na nuni da cewa Najeriya na samun koma baya a yakin da take da cin hanci da rashawa.

Kungiyoyin sun ce matsayin Najeriya a mizanin kasashen da cin hanci da rashawa ya yi wa katutu, ya kara faduwa kasa da maki biyar.

Najeriya na matsayin na 154 daga cikin jerin kasashe 180.

Kungiyar CISLAC dake kula da rashen kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Transperancy Internation a Najeriya ita ta kaddamar da wannan rahoto inda ta bayyana cewa Najeriya ta na dauke da maki 24 cikin 100.

Binciken dai ya yi nuni da cewa an samu rauni a yakin da ake yi na cin hanci da rashawa a kasar a shekarar 2021, idan aka kwatanta da shekarar 2020.

“A wannan rahoto da ya nuna mana kan cewa akwai matsalolin cin hancin da rashawa da suke kara karuwa a Najeriya, yanzu haka kamar yadda aka kwantanta kasashe da aka auna cin hanci da rasahwar da ke faruwa a ma’aikatun gwamnati a cikin kasashe 180 Nagjriya ta zo na 154.” In ji Awwal Musa Rafsanjani, shugaban kungiyar a Najeriya.

To ko mene ne illar da hasashen rahoton da kungiyar Transparency international ta fitar ke nuni. Hajiya Hadiza Sani Kangiwa na daya daga cikin manyan mambobin kungiyar ta CISLAC.

“Ja bayan da Najeriya ta yi ana samun matsaloli na cin hanci da rashawa sun karu ba wai ana nufin cewa hukumomi masu yaki da cin hanci da rashawa ba sa aiki ba ne, ba su ake nufi ba.”

Kwararre a fannin ci gaban kasa kuma jigo a jam’iyyar APC Dakta Ibrahim Dauda Bello ya bayyana cewa akwai abubuwa dama da suka kamata a yi la’akari da su a ayyukan da wannan gwamnati ke yi.

Sakamakon binciken dai na zuwa ne adaidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalolin rashin tsaro a fadin kasar da rashin ayyukan yi da kuma bankado wasu ayyukan jami’an gwamnati na sama da fadi da kudaden al’umma

Kazalika akwai binciken da yan’jarida suka gudanar da dai sauransu, duk kuwa da ikirarin da gwamnati kasar ke yi na cewa ta na yaki da ayyukan cin hanci da rashawa.

Hukumomin Najeriya dai na cewa suna iya bakin kokarinsu wajen aki da matsalar kuma a lokuta da dama sukan samu nasarar gurfanar da wadanda aka samu da laifi a harkar cin hanci da rashawar.

XS
SM
MD
LG