Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Cin Hanci Da Rashawa Barazana Ce Ga Tsaro


Shugaban Amurka Joe Biden

Saboda matsalar cin hanci da rashawa barazana ce kai tsaye ga tsaron kasar Amurka, yakar wannan masifa da ta addabi duniya ita ce babbar manufar tsare-tsaren cikin gida da kasashen waje na gwamnatin Biden-Harris.

Saboda haka, a ranar 3 ga Yuni, Shugaba Joe Biden ya ba da Takardar Nazarin Tsaro ta Kasa game da Yaki da Cin Hanci da Rashawa, don haka ya kafa yaki da cin hanci da rashawa a matsayin babbar manufar tsaron kasa ta Amurka. Yarjejeniyar ta umarci manyan jami'an gwamnati da su samar da dukkanin dabarun gwamnati don shawo kan wannan annoba.

Cin hanci da rashawa wata annoba ce da ta shafi duniya baki ɗaya wadda ke wawushe tsakanin kashi 2 zuwa 5 na kudaden da ake samu a cikin gida. Ko da yake babu wata ƙasa a duniya da ba ta da cin hanci da rashawa, amma tsananin cin hanci da rashawa ita ce mafi girma a kan mutanen da suka fi rauni a duniya. Sau da yawa, illar wannan matsala kan bayyana a kasashen da ba su da galihu, inda za a ga lamarin na shafar samar da kayayyakin more rayuwa na al’uma ko fannin kiwon lafiya. Kamar kuma yadda shugabar hukumar USAID mai raya kasashe ta lura Samantha Power ta lura, matsalar cin hanci da rashawa na barnatar da dala biliyan 1.26 a duk shekara a kasashe masu tasowa.

"Karfafa ƙarfin juriyar dimokiradiyya mai mutunta haƙƙoƙi na ɗaya daga cikin ƙayyadaddun ƙalubalen zamaninmu," in ji Shugaba Biden a cikin wata sanarwa da aka fitar akan Takardar Nazarin Tsaron Kasa kan Yaki da Cin Hanci da Rashawa.

“Cin hanci da rashawa na cinye tushen kasashen da suka rungumi tsarin dimokiradiyya. Yana sanyawa gwamnati rashin tasiri, ɓarnatar da dukiyar jama'a, da kuma sanya rashin daidaito wajen samun ayyuka, yana sanya wa iyalai wahala wajen wadatar da ‘ya’yansu. Cin hanci da rashawa na kawo cikas ga cibiyoyin dimokiradiyya, yana ingizawa da kuma tsaurara tsattsauran ra'ayi, kuma yana saukakawa gwamnatocin kama-karya su lalata tsarin dimokiradiyya.”

“Kasar Amurka za ta yi jagora tare da hadin gwiwa da kawayenta, kungiyoyin farar hula, da kamfanoni masu zaman kansu don yaki da matsalar rashawa. Amma wannan manufa ce ga duk duniya. Kuma, dole ne dukkanmu mu tashi tsaye wajen tallafa wa jajirtattun 'yan ƙasa a duniya waɗanda ke neman gaskiya, da gudanar da mulki cikin gaskiya, "in ji Shugaba Biden

Tabbas, Yarjejeniyar ta nuna cewa kamfanoni masu zaman kansu suna da muhimmiyar da rawa da za su taka a wannan yaƙin. Gwamnatin Amurka za ta kara dokar lauyoyi ga kamfanonin Amurka, tana bukatar su don inganta bayyanannen ayyukansu na harkokin waje, su yi aiki mafi kyau wajen raba bayanai tare da gwamnati, sannan su kai rahoto ga Sashen Baitul malin masu amfanar da su - wato, wadanda ke amfana da girbe fa'idar mallaka koda kuwa taken mallakar doka na wani ne.

“Yaki da cin hanci da rashawa ba wai abu ne da ya shafi shugabancin na kwarai kadai ba, mataki ne na kare-kai. Kishin kasa ne kuma yana da muhimmiyar rawa wajen raya dimokradiyyarmu da tabbatar da makomar.”

XS
SM
MD
LG