Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Ake Kai wa Ma’aikatan Agaji


Sudan ta Kudu, wacce ta sami 'yancinta daga Sudan a shekarar 2011, a mafi yawan kasancewarta, ta fuskanci kalubale iri-iri da suka jefa al’umarta cikin wahala.

Shekaru ashirin na rikici tsakanin arewa da kudu, talauci, da ci gaba da tashin hankali tare da Sudan, wanda ya hada da dakatar da fitar da mai a shekarar 2012 ya kuma lalata tattalin arzikin Sudan ta Kudu tare da dagula al’amura da raunana kasar da gwamnati.

A sakamakon haka, gwamnatin Sudan ta Kudu ba ta iya tunkara matsalolin cikin gida da bala'o'i da ke faruwa. Bugu da ƙari, ambaliyar ruwa, fari, da kuma rikice-rikicen cikin gida na sama da shekaru bakwai sun katse ayyukan noma da kiwo da kasuwanci, lamarin da ya kara dagula matsalar karancin abinci da jefa jama’a cikin yanayi na wahala.

A yau, Kudancin Sudan ta dogara sosai da tallafin da kungiyoyin kasashen wajen samun abinci, ababen more rayuwa, da kiyaye zaman lafiya, gami da kariya da kai dauki ga matan da aka ci zarafinsu.

Daga cikin mutum miliyan 12 da Sudan ta Kudu take da su, wasu kimanin miliyan 8.3 ko kuma kashi 70 cikin 100 na yawan mutanen za su bukaci agaji ko taimakon abinci na gaggawa a 2021, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Hakazalika, "Kudancin Sudan na daga cikin kasashe mafi hadari ga masu ga masu ayyukan agaji," in ji mai kula da USAID, Samantha Power a cikin wata sanarwa kwanan nan. "Tun daga farkon shekarar 2020, an kai hari kan ma'aikatan agaji sama da 400, a cewar Majalisar Dinkin Duniya." Wannan ya hada da kisan wasu ma’aikatan agaji biyu a watan Mayun 2021.

"Kasar Amurka ta yi Allah wadai da wannan tashin hankali kuma ta yi kira ga Gwamnatin Sudan ta Kudu da ta kare fararen hula da masu ayyukannjin-kai tare da kame wadanda suka aikata hakan a Renk, Torit, da Jamjang tare da hukunta su," in ji Power.

“Kai hari akan ma’aikatan agaji, na jefa rayukansu cikin hadari; yana kuma kawo cikas ga gudummawar da ake ba mabukata. Hare-haren na baya-bayan nan sun tilasta wa wasu kungiyoyi dakatar da taimakon jin kai a yankunan Unity da Upper Nile, wadanda ke dab da fadawa kangin matsananciyar yunwa, ma’ana kusan mutum 45,000 na iya rasa damar samun taimakon da suke matukar bukata, ”inji ta.

“Abokan huldarmu masu ayyukan jin-kai na aiki ba tare da gajiyawa ba kuma a cikin kasada don isar da taimako. Kula da amincin su da samun damar shiga wuraren mabukata yana da mahimmanci don ceton rayukan mutane. Hare-hare, tursasawa, ko barazanar da ake yi wa ma'aikatan agaji, ba tare da la'akkari da ƙasar da suka fito ba, ba za a amince da su ba.

"Wajibi ne Gwamnatin Sudan ta Kudu ta dauki kwararan matakai cikin gaggawa don kare ma'aikatan jin kai da kuma samar da ci gaba ba tare da wata matsala ba ga wadanda ke fama da matsalar karancin abinci da sauran bukatun na yau da kullum.”

XS
SM
MD
LG