Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Cin Hanci a Nijar Ta Zama Gama-Gari - Hukuma


Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijar, Mai Shari'a Abdurrahman Gousman

Yau 9 ga watan Disamba, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakarwa kan muhimmancin yaki da cin hanci a duk fadin duniya.

Yayin da kasashen duniya ke bukukuwan ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin ranar yaki da cin hanci, hukumar yaki da cin hanci a Jamhuriyar Nijar ta bayyana dalilan siyasa a matsayin wata hanyar da ke kara dagula yaki da wannan matsala.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci a kasar, Mai Shari’a Abdurrahman Gousman, ya ce, ma’aikatun gwamnati suke kan gaba wajen yawan karbar cin hanci.

Ya kara da cewa duk da irin nasororin da ake samu, har yanzu “akwai sauran rina a kaba.”

Baya ga ma’aikatun gwamnati a cewar Gousman, jam’iyun siyasa su ne na biyu a sahun karbar cin hanci sai kuma kungiyoyin fararen hula.

Mataimakin hukumar, Salisu Ubandoma, ya ce yaki da cin haci da rashawa, wani lamari ne da ke bukatar hadin kan kowa da kowa.

“A da, inda ba a samun cin hanci shi ne cikin makaranta ko kuma fannin likita, (Asibiti) to amma yau matsalar ta zama gama gari, ko in aka je akwai cin hanci da rashawa.” Inji Ubandoma, a lokacin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG