Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Tsaro Na Shafar Safarar Kayan Gona Zuwa Kudancin Najeriya


Kayan Gwari

Matsalar rashin tsaro a arewacin Najeriya ta kawo koma baya ga kasuwancin kayan gwari a kudancin kasar, abin da ya sa ‘yan kasuwar jihar Lagos suka fara rangadin jihohin arewa suna lallashin manoma.

Rangadin dai ya fara ne a jihar Sokoto, inda ‘yan kasuwar suka hadu da manoma daga jihohin Kebbi da Zamfara suka tattauna matsalolin.

Aiyukan ta'addanci da suka hana manoma zuwa gonakin su, da yawan satar mutane akan hanya na daga cikin manyan matsalolin da suka addabi manoma da ‘yan kasuwa, har ma da shafar harkar sufurin kayan gwari zuwa kudancin Najeriya.

Haka kuma, kisan da aka yiwa manoma a jihar Borno ya kara jefa tsoro cikin zukatan manoma, ga kuma ambaliyar ruwa da aka samu lokacin damuna a arewacin Najeriya, wadda ta kara hana yin noman kayayyaki balle ta kai ga sufurin su zuwa Kudu.

Aliyu Mai Tasamu Isa, shine shugaban kungiyar masu noma da sayar da albasa ta Najeriya ya ce, ko bayan wadannan matsalolin na rashin tsaro akwai wasu kalubale dake tarnaki ga yawaitar kayan har a kai su wani wuri.

Alhaji Dauda Sulaiman jigo, babban manomi ne kuma mai kasuwancin Tattasai da Tarugu ya ce akwai bukatar hukumomi su mayar da hankali ga matsalolin da ke tarnaki ga manoman kayan gwari saboda muhimmancin da suke da shi.

Jihohin arewacin Najeriya, suna sahun gaba wajen samar da kayan gwari da ake amfani da su a Najeriya da ma wasu kasashen Afirka.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Muhammad Nasir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00


An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG