Kawayen Amurka a kasashen Turai sun cimma matsaya mabanbanta da Amurka akan bayanin da Prime Ministan Israila Benjamin Netenyahu ya gabatar, akan dalilin da ya bayar cewa kasar Iran ta shirga karya game da shirin ta na Makakan Nukiliya.
Shugaban na Israila ya danganta zargin nasa ne akan wani kundi mai shafuka dubu 55 da faifan CD har 183 dake kunshe da bayanan sirri da hukumar tattara bayanan sirri ta kasar sa ta samu daga wani wuri a babban birnin kasar Iran ,Tehran.
Yanzu haka dai Ministan harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson ya bi sahun takwarorin sa na kasashen Turai a jiya Talata, inda yake kare yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015 da kasar ta Iran, wanda yanzu ya rage wa shugaba Trump ya yanke shawara daga nan zuwa sha biyu ga wannan watan na kodai ya sabunta wannan yarjejeniyar ko kuma ya yi watsi da ita
Facebook Forum