Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Koriya Ta Kudu na so Majalisar Dinkin Duniya Ta Sa Ido Akan Rufe Cibiyar Nukiliyar Makwabciyarta


Shugabannin yankin Koriya

Jami’an koriya ta kudu sun fada ranar Lahadi cewa Kim ya shirya zai gayyaci kwararru, da ‘yan jarida daga koriya ta kudu da Amurka don su kasance wurin a lokacin da za a rufe cibiyar.

Shugaban koriya ta kudu Moon Jae-in ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta sa ido a lokacin da koriya ta arewa ke rufe cibiyar gwajin makaman nukiliyarta dake Punggye-ri.

Wani mai magana da yawun Moon ya fada yau Talata cewa shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana ta wayar tarho da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.

Shugaban koriya ta arewa Kim Jong Un ya yi alkawarin rufe cibiyar a karshen watan nan na Mayu.

Wannan cigaba da aka samu na zaman wani bangaren matakan diflomasiyya da suka hada da wani babban taro da aka yi tsakanin Moon da Kim da kuma shirin ganawar da ake yi tsakanin Kim da Donald Trump.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG