Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsugunin Jami'a Ya Jawo Cecekuce a Jihar Gombe


Kofar jami'a
Kofar jami'a

Kowace jiha tana da jami'ar gwamnatin tarayya a babban bininta to sai dai na jihar Gombe baya cikin babban birnin jihar.

Yayin da shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya je bude taron habbaka tattalin arewa maso gabashin kasar da aka yi makon jiya a Gombe babban birnin jihar Gombe, mai martaba sarkin Gombe Alhaji Shehu Usman Abubakar ya roki shugaban da ya dage jami'ar gwamnatin tarayya daga Kashere zuwa Gombe.

Bukatar da sarkin Gome ya mika wa shugaban kasa ta jawo cecekuce tsakanin al'ummar jihar. Malam Ibrahim Adamu Mohammed shugaban dandalin Lamurde a Gombe ya ga ya kamata a sake matsugunin jami'ar domin ya dace da hankali domin babu masauki a Kashere wani kuma idan ya je garin sau daya baya sake komawa. Ya ce irin wannan asara ce ga jihar Gombe idan ana batun cigaba sabili da ganin haka ya sa sarkin Gombe ya nemi a sake wa jami'ar matsuguni.

Kodayake jami'a na kawo cigaban da aka kaita ba jami'a garin ke bukata ba domin cigaba. Wurin ruwan sha da ayyukan gona da kananan makarantu yake bukata.Malam Ibrahim ya ce duk wasu ka'idodi da ya kamata su cika a sake wa jami'ar matsuguni zasu cika.

To sai dai dan majalisar dattawa daga jiharUsman Bello Kumo ya ce dokace ta kafa jami'ar tare da matsuguninta. Ya ce a matsayinsa na dan majalisar dattawa dake wakiltar Ako da ma inda jami'ar take hakin shi ne ya kare duk abun da zai kawo ma mazabarsa cigaba. Maganar sake wa jami'ar matsuguni ba haki ba ne na shugaban kasa. A'a haki ne da ya rataya a wuyan majalisa. Ya ce sun riga sun yi doka da ta kafa jami'ar da suka kira Jami'ar Gwamnatin Tarayya A Garin Kashere. Babu wanda ya isa ya sake mata matsuguni sai an sake komawa gaban majalisa.Sabo da haka zauren majalisa za'a kai koken a ce a canza. Dan majalisar ya ce kada ma a cigaba da wannan zancen domin idan an tunzura talakawa ba za'a ji dadi ba. Ya ce ba zasu yadda a kawo masu abu na cigaba ba kana a ce za'a sake daukeshi. Yin hakan zai haifar da abu mara dadi.

Abdulwahab Muhammed nada karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG