Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matukar A Na Son Garambawul A Najeriya Sai An Zakulo ‘Yan Takarar Da Ba Su Da Bashin Ramuwa- Yunusa Tanko


YUNUSA TANKO
YUNUSA TANKO

Yayin da masu sha’awar takarar shugabancin Najeriya a badi ke kara bayyana muradin su, tsohon shugaban zauren jam’iyyu Yunusa Tanko ya ce za a iya samun garambawul ga tsarin shugabancin Najeriya.

Tanko na magana ne a taron da wasu sanannun ‘yan siyasa su ka kira don duba sabbin fuska da su ke ganin ya dace a gwada su a kan madafun iko a babban zaben mai zuwa.

Yunusa Tanko wanda ke jagorantar jam’iyyar NCP da marigayi lauya Gani Fawahinmi ya kafa, ya ce Najeriya na bukatar sabon salon siyasa don kaucewa yanda ya ce aka kawo Obasanjo a 1999 don wanke fusatar magoya bayan Abiola da aka soke zaben sa a 1993 kazalika ya kasance ya na kullace da marigayi Janar Abacha wanda ya tura shi gidan yari da tuhumar juyin mulki.

Duk da Tanko bai ambaci sunan shugaba Buhari ba, ya ce wadanda su ka dade su na jan ragamar Najeriya a soja da farar hula sun kure wa’adin damar su ta iya dawo da Najeriya kan turba.

A na sa bangare tsohon ministan matasa da wasanni Solomon Dalung ya yi wasu tambayoyi ne kan yanda ya ke ganin za a sha wuya wajen yi wa talakawa kamfen da alkawuran da a baya ba a samu cikawa ba.

Zuwa yanzu dai ba a tsira daga batun damar ‘yan arewa ko ta ‘yan kudu wajen amsar ragamar mulki ba maimakon a ce za a iya samun dan takara mai tsayawa don cancantar sa kadai.

“Ba bangaren shugaban kasa ba ne kadai ya gaza, ka je ka duba shugaban karamar hukumar ka, za ka taras ba zai rika zagawa ya na duba inda a ka samu ramuka kan titi don a cike su ba, amma tunanin sa shi ne yanda za a samu kudi don bukukuwa ko raka gwamna taruka” inji Barista Adewole Adebayo daga jihar Ondo da ke cikin maso son takarar shugaban kasa a 2023.

Barista Adebayo ya cigaba da cewa za ka ga ministoci na zuwa taron majalisar zartarwa duk laraba don ba da kwangiloli amma ba mai iya tambayar inda a ka kwana a kwangilolin da a ka bayar a baya. Ya zama mai muhimmanci ‘yan Najeriya su kawar da bambance-bambancen kabilanci, wariya don addini da yanki matukar kasar za ta tsira daga talauci, rashin tsaro da guguwar ‘yan a fasa kowa ma ya rasa.

Zuwa yanzu dai a na sa ran gudanar da babban zaben a ranar 23 ga watan febrerun badi tun da alamu na nuna an daidaita kan sabuwar dokar zabe tsakanin shugaba Buhari da majalisar dokoki.

XS
SM
MD
LG