Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan al-Shabab Sun Kaiwa Jerin Gwanon Motoci Hari a Kenya


Farar hula a kalla ‘daya ya rasa ransa kuma jami’an ‘yan sanda da yawa sun raunata a wani hari da ake zargin ‘yan kungiyar al-Shababa sun kaiwa wani jerin gwanon motoci a gabashin Kenya, a cewar ma’aikatar harkokin cikin gida.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida, Mwenda Njoka, ya ce harin ya faru ne jiya Asabar alokacin da jerin gwanon manyan motoci da ‘yan sanda ke baiwa kariya ke tafiya daga yankin Lamu akan gabar arewacin Kenya dake kusa da Somaliya.

Njoka ya ce “wasu gungun mutane da ake zargin mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta al-Shabab ne suka kai harin, wanda ya lalata motocin ‘yan sanda biyu. Shugaban ‘yan sandan yankin Larry Kieng ya ce maharan sun harba roka ne kan motocin ‘yan sandan, inda motoci suka kama da wuta.

Mayakan al-Shabab sun sha kai hare-hare a yankin da aka kai harin a shekarun baya-bayan nan. Al-Shaban na da alaka da al-Qaida, kungiayr da Osama bin Laden ya kafa a shekarar alif 988.

Gwamnatin Kenya ta yi ta kokarin dakatar da hare-haren da ‘yan kungiyar al-Shabab ke kaiwa, wadanda suka ce suna ramuwar gayya ne bayan da Kenya ta aika da sojojinta zuwa Somaliya a shekarar 2011 a wani bangare na sojojin kungiyar tarayyar Afirka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG