Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Al-shabab Sun Kwace Wani Sansanin Soja a Somalia


Al-shabab

A Somalia, mayakan Al-shabab sun kwace wani sansanin sojojin kasar dake wani wuri da ake kira Laanta Buur, a wani tsohon fursina dake tazarar kilomita 40 a yammacin birnin Mogadishu, kamar yadda jami'amn kasar suka yi bayani.

Mayakan sakan sun kai hari kan sansanin ne da misalin karfe 1:30 a daren litinin din nan, suka kashe sojoji suka kuma kwace makamai da manyan motocin soja, akamr yadda aka ji daga bakin jami'an tsaro.


An fara kai harin ne da kunar bakin wake da wata motar da aka dankarawa nakiyoyi a kofar shiga sansanin, sannan daruruwan maharan da muggan makamai suka bude wuta. An ce wasu sojoji a sansanin sun so su kare kansu, amma 'yan binidgar sun ka fi karfinsu.


A wani jami'in tsaro yace an kashe akalla sojoji uku, amma jami'an kasar suna fargabar hasarar zata fi haka.

Jami’in da yayi bayani kan harin yace ba a dade da kafa wasu cibiyoyi a sansanin ba da suka hada da Lower Shabelle da Middle Shabelle da Banadir. Babu kuma tabbacin ko an kashe wani babban jami’in soja ko kuma an raunata shi a harin da aka kai.

XS
SM
MD
LG