Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Barin Wuta a Birnin Juba Na Sudan Ta Kudu


Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir

An sake samun barkewar barin wuta a babban birnin Sudan ta Kudu, biyo bayan rikicin da ya shafe kwanaki ana yinsa da ‘yan adawa, wanda ya yi sanadiyyar kashe fiye da mutane 100.

Shedu a Juba sun ce jiya Lahadi harbe harben ya watsu a bangarori da dama na birnin a musayar wutar da aka yi tsakanin ‘yan tawayen da jami’an tsaron gwamnati.

A baya dai ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kira don tausasar ‘yan Sudan ta Kudun bayan wani kazamin fadan da aka tafka a ranar jajibirin bikin ranar ‘yancin kasar.

Inda takardar da Amurkan ta fita ta yi kira ga mayakan da ke marawa Shugaba Salva Kiir baya da kuma ‘yan tawayen da ke goyon bayan mataimakinsa na farko Riek Machar da su sasanta a tsakaninsu.

Hatta kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya sun yi alla-wadai da wannan rikicin da yaki ci ya ki cinyewa a birnin na Juba. Ciki har da hare-haren da aka kaiwa wasu jami’an diflomasiyya na Majalisar Dinkin Duniya a Juba a ranar Alhamis da ta gabata.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG