Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Kurdawa Na Samun Nasara A Kokarn Kwato Birnin Mosul


Shugabannin Kurdawa sun ce suna samun nasara sakamakon hare haren da sojojin Iraqi suka fara kaiwa, wanda aka dade ana hasasen kaisu don sake kwato birnin Mosul dake Arewacin kasar da ya dade hannun kungiyar ISIS.

Shugaban Kurdawa Masoud Barzani a wani taron yan jarida da aka nuna a tashoshin telbijin a jiya Litinin yace an yi nasarar akalla kilomitoci 200 a cikin kwana daya kacal da fara wannan barin wuta.

Wannan dai shine farmakin sojin mafi girma tun bayan da rundunar Amurka ta fice daga kasar shekaru biyar da suke wuce, sai dai wannan hare haren na janyo fargaba a kan lafiyar dubban fararen hula dake zaune a yankin.

Wannan yunkurin sojin na ‘yanta birnin Mosul daga IS na hadin-gwiwa ne da ya hada hancin rundunonin sojan Kurdawa da yan sandan tarayya da mafarautan Sunni da kuma mayakan yan Shi’a. Rundunar hadin guiwa karkashin jagorancin Amurka da suka share tsawon shekaru biyu suna fatatakar mayakan ISISI daga sama a Iraqi da Syria su ma suna cikin wannan fafatikar da ake ta ‘yanttarda birnin na Mosul.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG