Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Na Neman Biliyoyin Daloli Don Yaki Da Coronavirus


Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bukatar karin makudan kudade idan ana so a kaucewa asarar rayuka sanadiyyar COVID-19 a duniya.

A yau Juma’a Majalisar Dinkin Duniya ta kara fadada kokon-bararta na neman taimako don magance mummunan tasirin da cutar COVID-19 ke yi kan fannin lafiya da kuma tattalin arzikin wasu sassan duniya da cutar ta fi kamari.

Majalisar ta kai adadin kudaden da take nema ne zuwa dala biliyan 10.3, inda ta yi gargadin cewa, kin daukan mataki a yanzu, zai iya sa a rasa rayuka bil-adadin da kuma kashe tiriliyoyin daloli a nan gaba.

Yayin wata hira da ya yi da manema labarai, shugaban sashen gudanar da ayyukan jin-kai na majalisar Mark Lowcock ya ce, “har sai mun dauki mataki yanzu, idan kuma ba haka ba, za a tafka asarar rayuka sama da abin da aka gani daga illar cutar.”

Tun a karshen watan Maris, Majalisar Dinkin Duniya ta da farko ta nemi taimakon dala biliyan biyu ($2B) saboda tallafawa wasu kasashe 40 wajen yin yaki da da cutar ta COVID-19, wacce sabuwar coronavirus ta haifar.

Yayin da kwayar cutar ta ci gaba da yaduwa, ta sake yin makamancin wannan kira na neman taimakon ($6.7B) a watan Mayu. amma ($1.6B) kadai ta samu na wadannan kudade.

Yekuwar neman taimakon a yau Juma’a wani yunkuri ne na tallafawa mutum miliyan 250 a kasashe 63 musamman a nahiyar Afirka, Gabas Ta Tsakiya da kuma yankin Latin Amurka.

Daga cikin sama da mutuum miliyan 13.6 da suka kamu da cutar ta COVID-19 a duk fadin duniya kashi daya cikin uku sun fito ne daga kasashen da Majalisar Dinkin Duniyar ke son ta taimakawa.

Daga cikin wadannan yankuna, Latin Amurka ne yanki da lamarin ya fi kamari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG