Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Zargi Gwamnatin Habasha Da Jefan 'Yan Gudun Hijira Cikin Hadari A Tigray


'Yan gudun hijira a yakin Tigray na kasar Habasha mai fama da yaki

Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ta bayyana fargaba a kan tilasatawa ‘yan gudun hijiran Eritrea komawa sansanonin da suka arce daga yankin Tigray na Habasha mai fama da tashin hankali.

Gwamnatin Habashan ta fada a wata sanarwa cewa zata maida ‘yan gudun hijiran Eritrear da suka arce daga Tigray zuwa Addis Ababa a cikin ‘yan makwanni masu zuwa. Hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD ta ce tana da labarin cewa an kwashe daruruwan ‘yan gudun hijira da bos bos zuwa Tigray.

Gwamnatin ta ce abin da zai kare lafiyar ‘yan gudun hijiran shine su koma sansanonin nasu, bayan da sojojinta suka murkushe mayakan masu biyayya ga tsohon shugaban kungiyar ‘yan tawayen yankin ta Tigray People’s Liberation Front.

Shugaban hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD Filippo Grandi ya fada a jiya Juma’a cewa yana cikin fargaba ganin ana maida ‘yan gudun hijiran zuwa yankin Tigray, inda ake hana hukumomin jin kai da wasu kungiyoyi isa wurin tun lokacin da aka fara yaki a ranar hudu ga watan Nuwamba.

Kimanin ‘yan gudun hijiran Eritrea dubu 96 ne ke zaune a sansanoni a yankin.

Hukumomin jin kai sun ce sun yi imanin cewa ana fama da rashin abinci a sansanoni kana sun nuna damuwa a kan rahotannin game da karuwan tashin hankali a wasu wurare na yankin.

Gwamnatin Habasha ta ce zata baiwa ma’aikatan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya da kawayenta damar shiga yankin Tigray.

Yayin da sanya hannu a kan yarjejeniya ne matakin farko, akwai bukatar aiwatar da yarjejeniyar ta yadda zata tabbatar da kare lafiyar ma’aikatan jin kai da kuma samun shiga bada wata matsala ba, kamar yanda sharudar aiki tsakanin da Allah da kaucewa rashin adalci suka gindaya, inji sanarwar Grandi.

XS
SM
MD
LG