Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Jega Yayi Ake Rade Radin Korarsa Daga Mukaminsa?


Farfesa Attahiru Jega
Farfesa Attahiru Jega

Kasancewar a bana za’a fara amfani a lokacin zabe da na’urar da zata tantance sahihancin kati da ake kiranta machine card reader a turance, kuma baban abin dake faruwa shine babu wani mai yin adawa da amfani da wannan na’urar kamar jam’iyyar PDP.

Dalilin jam’iyyar shine ba’a taba gwada na’urar ba anga cewar tana aiki ko batayi, kuma idan akazo lokacin zabe kuma aka samu tangarda to ya za’ayi batun zabe tunda ba’a taba gwada taba. Sai kuma batun batirin ita wannan na’ura wadda tana iya rike caji na awa takwas ne kawai, idan har mutane suka fito zabe suka hau kan layi aka samu matsala ba’a fara jefa kuri’a da wuri ba har awa takwas tazo ta shige, to ya za’a yi da mutane? zasu jefa kuri’a ko bazasu jefa ba.

Wannan batu dai na daya daga cikin batun da yake kawo takaddama tsakanin jam’iyyar PDP da kuma shi shugaban hukamar zabe mai zaman kanta.

Idan ba’a manta ba a baya, jawabin da Edwin Clark jagoran ‘yan Niger Delta, wanda ya kira manema labarai yake bayyana cewa Attahiru Jega ya hada baki da kungiyar dattawan arewa ana zuwa ana ‘daukar matasa wanda shekarunsu bai kai ba ana musu rijista, domin kawai a kara yawan masu jefa kuri’a na arewacin Najeriya, ta yadda zasu fi na sauran sassan kasar. Ya kuma nemi da a kori Jega har ma a gurfanar da shi a gaban kotu.

Jam’iyyar adawa dai sun fito suna fadin cewar ya kamata jama’a suyi hattara game da wannan batu na cire shugaban hukumar zaben Najeriya, har ma akwai wadanda suke son zuwa kofar ofishin hukumar zaben su rika yin zanga zanga, game da wannan batu suna kuma fadin cewar wata makarkashiya ce da akeyi, dama ana so ayi magudi ne a na kuma ganin idan ya kasance a gurin wata kila baza a iya yin magudin ba, shiya sa ake yin wannan tunanin yadda za’a cireshi a maye gurbinsa da wani.

XS
SM
MD
LG