Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Ke Kashe Giwaye a Botswana?


Wata giwa da aka samu a mace a Botswana
Wata giwa da aka samu a mace a Botswana

Gwamnatin Bostwana tana bincike game da karuwar adadin giwayen da ke mutuwa wanda aka kasa gano dalili.

Adadin ya karu zuwa 275 wanda ya haura 154 da aka gani cikin mako biyu da suka gabata, kamar yadda gwamnatin kasar ta fada jiya Alhamis.

An fara ganin giwayen da suka mutu ne cikin watannin da ysuka gabata a yankin da ake kira Okavango Panhandle, kana hukumomin sun ce sun dukufa wajen kokarin gano abin da ke kashe giwayen.

Tuni dai an tabbtar cewa mutuwar giwayen ba ta da nasaba da masu farautar hauren dabbobin, saboda akan tsinci mushensu ne da cikakkun sassan jinkinsu.

Sai dai wata sanarwa da Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun kasa da yawon bude ido ta fitar, ta ce “dakunan bincike uku a Zimbabwe, Afirka ta Kudu da Canada aka zaba su duba samfurin da aka dauka na matattun giwayen.”

A cikin rahoto da aka shiryawa gwamnati da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya gani, kungiyar da ke kare giwaye ta kasa da kasa wato “Elephants Without Borders” da ake kira (EWB) a takaice, ta ce wani bincike da suka gudanar ta sama ya nuna cewa giwayen masu shekaru daban-daban ne ke mutuwa.

Cikin wani rahoto kungiyar ta ce ta kidaya giwa 169 da suka mutu a ranar 25 ga watan Mayu sannan ta kidaya wasu 187 daban da su ma suka mutu a ranar 14 ga watan Yuni.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG