Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Ta Je Yi A Ghana?


Nancy Pelosi

Shugabar majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi da tawagarta sun isa Accra, babban birnin kasar Ghana domin halartar wani gagarumin bikin tunawa da fataucin bayi da aka yi shekaru 400 da suka wuce, wanda aka yi wa take da “Shekarar Komawa Gida”.

Jakadiyar Amurka a Ghana Stephanie S. Sullivan, da kakakin majalisar dokokin Ghana Farfesa Mike Oquaye ne suka tarbi Pelosi da tawagarta a filin saukar jiragen sama na kasa da kasan a jihar Accra a jiya Lahadi.

Wannan gagarumar tawaga za ta yi tattaunawa ta musamman da shugaba Nana Akufo-Addo, kuma Pelosi za ta gana da takwaran aikinta na Ghana.

Da take yi wa manema labarai karin bayani a kan wannan ziyarar, ministan harkokin wajen Ghana kuma ‘yar majalisa mai wakiltan mazabar “Anyaa Sowutuom” Shirley Ayorkor Botchwey ta ce, wannan ziyara da Nancy Pelosi da babbar tawagarta mai mambobi 35 zuwa 40 za ta haska Ghana a idon duniya, kuma za ta karawa bikin "komawa gidan armashi," saboda zai janyo hankali a kan kasar Ghana.

A kan wannan bikin "dawowa gida," Ghana tana sa ran ganin dubun dubatan mutane daga kasashen duniya masu alaka da nahiyar Afrika.

Daga cikin wuraren da Pelosi za ta kai ziyara, akwai tashoshin jigilar bayi ta Cape Coast Castle, da ta Elmina Castle da yanzu suka zama gidajen tarihi.

A Cape Coast Castle tawagar za ta je kofar da ake shigewa da bayi da aka yi wa lakabi kofar da ba a dawowa, wato "Door of No Return" a turance.

Kafin wannan ziyara Pelosi ta ce za su kai wa shelkwatar sojojin Amurka a Afirka ziyara, inda za su ji daga jami’ai sannan su yaba musu.

‘Yan Ghana da dama ne suka bayyana farin cikinsu da wannan ziyara da tawagar Amurka ta kai karkashin jagorancin shugabar majalisar wakilan Amurka Pelosi.

Da yammacin yau Litinin za a shiryawa Pelosi da tawagarta liyafar ban girma a fadar shugaban kasar Ghana ta Jubilee House a jihar Accra.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG