Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ronaldo Ya Sanar Da Juventus Cewa Yana So Ya Tafi


Cristiano Ronaldo yayin wani taron manema labarai (Foto: UEFA via REUTERS)

Hakan ya biyo bayan tayi da Manchester City ta yi masa a ranar Laraba na kwantiragin shekara biyu akan kudi euro miliyan 15.

Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya fadawa kungiyarsa cewa yana so ya tafi a cewar shafin wasanni na Sky Italiya.

Hakan ya biyo bayan tayi da Manchester City ta yi masa a ranar Laraba na kwantiragin shekara biyu akan kudi euro miliyan 15.

Sai dai Juventus ta ce ba za ta rabu da dan wasan dan asalin kasar Portugal mai shekaar 36 ba, har akan kudi euro miliyan 25.

Sai a baya-bayan nan Ronaldo ya sanar da kungiyar ta Juventus burins na tafiya yayin da rahotanni a baya suka nuna cewa bai sanar da su ba.

Kwantiragin Ronaldo a Juventus da ke gasar Serie A a Italiya zai kare ne a watan Yunin 2022 amma yana da damar da zai iya tafiya idan yana so kafin a rufe kasuwar sayar da 'yan wasa.

A lokacin yana gasar ta Premier a Ingila, Ronaldo ya zura kwallaye 118 a wasannin 292 a lokacin yana kungiyar Manchester United a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2009.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG