Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mece Ce Makomar Mbappe Da Pochettino A PSG?


Mbappe, hagu, da mai horar da 'yan wasan PSG Pochettino, dama
Mbappe, hagu, da mai horar da 'yan wasan PSG Pochettino, dama

Duk da cewa kungiyar ta lashe gasar Ligue 1 a karshen makon da ya gabata, hakan bai hana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan tafiyar Pochettino ba.

Mai horar da ‘yan wasan Paris Saint Germain Mauricio Pochettino da dan wasansa Kylian Mbappe, ya yi ikirarin cewa suna nan daram-dam a kungiyar, babu inda za su je.

An dai jima ana ta yamadidin cewa Pochettino zai bar kungiyar ta PSG tun bayan da aka fitar da ita a gasar cin kofin nahiyar turai ta UEFA a zagayen ‘yan 16.

Duk da cewa kungiyar ta lashe gasar Ligue 1 a karshen makon da ya gabata, hakan bai hana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan tafiyarsa ba.

Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ruwaito cewa, ana raderadin cewa mai horar da ‘yan wasan Tottenham Antonio Conte ne zai maye gurbin Pochettino, dan asalin kasar Argentina.

A gefe guda kuma, kwantiragin Mbappe zai kare a lokacin bazara da ke tafe, shi ma kuma ana ta ci gaba da maganar cewa zai koma Real Madrid.

Sai dai kamar yadda AP ya ruwaito, Pochettino ya ce, a halin da aka ciki, shi da Mbappe suna nan daram a kungiyar har kakar wasa mai zuwa.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG