Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Messi Ba Zai Buga Wasan PSG Da Brest Ba

Messi a tsakiya daga baya, a lokacin suna atisaye

A farkon watan nan, Messi ya yi ban kwana da kungiyar Barcelona da ya kwashe tsawon shekara 21, inda ya yi ta zub da hawaye a wani taron manema labarai da aka shirya don yi ban-kwana da shi.

Rahotanni daga Faransa na cewa sabon dan wasan Paris Sainte-Germain Lionel Messi ba zai buga wasan kungiyar da za ta kara da Brest a ranar Juma’a ba.

Hakazalika, bayanai sun yi nuni da cewa shi ma Neymar ba ya cikin tawagar ‘yan wasan da za su kara da Brest.

Rahotanni sun ce Messi bai kammala yin atisaye ba, saboda rabon da ya buga kwallo tun da suka lashe kofin Copa America da Argentina ta ci bayan doke Brazil da ci 1-0.

An gabatar da shi ne gabanin kungiyar ta buga wasanta da Strasbourg wacce ta lallasa da ci 4-2 a ranar Asabar.

Yanzu haka magoya bayan kungiyar ta PSG sai sun jira nan da zuwa 29 ga watan Agusta inda PSG za ta kara da Reims kafin su ga taka ledar Messi mai shekara 34.

A farkon watan nan, Messi ya yi ban kwana da kungiyar Barcelona da ya kwashe tsawon shekara 21, inda ya yi ta zub da hawaye a wani taron manema labarai da aka shirya don yi ban-kwana da shi.

A karon farko, Messi ya nuna sabuwar rigar wasan kwallonsa ta PSG

A karon farko, Messi ya nuna sabuwar rigar wasan kwallonsa ta PSG
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG