Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Michelle Obama Na Taya Hillary Clinton Yakin Neman Zabe


Michelle Obama da Hillary Clinton suna kamfe
Michelle Obama da Hillary Clinton suna kamfe

A karon farko a tarihin siyasar Amurka, jiya matan shugaban Amurka guda biyu da suka hada da matar wani tsohon shugaban kasa tazo ta hade da matar shugaban kasa mai ci yanzu, sun hada karfi suna kyamfe mai alaka da zaben wannan shekarar na shugaban kasa.

Hakan ta faru ne a garin Winston-Salem dake jihar North Carolina a jiya Alhamis lokacinda Michelle Obama, matar shugaba Barack Obama mai ci yanzu, ta bayyana don yin jawabin nemarwa Hilary Clinton, matar tsohon shugaba Bill Clinton, kuri’u a gwagwarmayar da Hilary din take yi na lashe zaben shugaban kasan wannan shekara.

Wannan jihar ta North Carolina dai tana daya daga cikin jihohin Amurka da dole sai dan takara ko ‘yar takara sun lashe su kafin suyi nasarar lashe zaben shugaban kasar.

XS
SM
MD
LG