Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mike Pence Ya Caccaki Joe Biden a Babban Taron 'Yan Republican


Yayin da tashe-tashen hankula masu nasaba da launin fata ke kara ta'azzara a Amurka, da daren jiya Laraba Mataimakin Shugaban kasa Mike Pence, ya shaida wa ‘yan kasa cewar “baku da matakan tsaro karkashin jagorancin Joe Biden.” Ya caccaki dan takarar jam’iyyar Demokrat din mai ra’ayi irin na masu bukatar rage kudaden ‘yan sanda.

“Joe Biden ya ce tsarin Amurka kansa na nuna wariyar launin fata ne,” a cewar Mike lokacin jawabinsa a babban taro n jam’iyyar Republican a dare na 3. Ya kara da cewa Biden ya ce 'yan sandan Amurka na nuna ma tsiraru banbanci a fakaice. Kuma da aka tambaye shi ko zai goyi bayan rage kudaden ‘yan sanda sai ya ce Lallai ba shaka zai yi.

Pence ya amince da tsayawa takara tare da Trump karo na biyu a zaben da za a gudanar a ranar 3 ga watan Nuwamba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG