Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mota Ta Kutsa Cikin Mutane a Dandalin Time Square


Dandalin Time Square a birnin New York.
Dandalin Time Square a birnin New York.

Wata mota ta banke mutane suna tafiya da kafa a dandalin Times Square, ta kashe wata mace ‘yar shekaru goma sha takwas jiya alhamis.

‘yan sanda sun bayyana matukin motar Ba’amurke dan shekaru ishirin da shida da suna Richard Rojas, wanda aka sha kamawa sabili da tuki a buge.

Wadansu mutane ishirin da biyu kuma sun ji rauni, bisa ga cewar ma’aikatar kashe gobara ta birnin New York. Hudu daga cikinsu suna cikin wani mawuyacin hali, sai dai ana kyautata zaton babu wanda zai raya ransa a cikinsu, biga ga cewar kwamishin ma’aikatar kashe gobarar ta birnin New York Daniel Nigro yayin wata ganawa da manema labarai.

Rundunar ‘yan sandan birnin New York dake aiki da hadin guiwar hukumar bincike manyan laifuka ta FBI wajen gudanar da bincike, yace, bbu alamar lamarin yana da alaka da ta’addanci, ana kuma ci gaba da bincike.

‘yan sanda sunce motar kirar Honda Sedan ta haura kan simintin masu tafiya da kafa da gudun gaske kafin ta rafkawa fal waya .

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG