Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mu Ne Muka Lashe Zabe, Za Mu Gabatar Da Hujjoji - Obi


Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi yayin taron manema labarai a Abuja, 02 Alhamis, 2023(Hoto: Facebook/Peter Obi)
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi yayin taron manema labarai a Abuja, 02 Alhamis, 2023(Hoto: Facebook/Peter Obi)

Obi ya ce za su bi duk wata hanya da doka ta tanada domin ganin sun kwato hakkinsu.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Labor Party a Najeriya, Peter Obi, ya ce za su bi hanyoyin da doka ta tanada don kwato nasarar da suka samu a zaben 2023.

A ranar Laraba, hukumar zaben Najeriya INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Tinubu ya samu kuri’a 8,794,726, abokin hamayyarsa na PDP, Atiku Abubakar ya samu kuri’a 6,984,520, sai Obi da ya zo na uku da kuri’a 6,101,533.

Sai dai yayin wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, Obi ya ce su ne suka lashe zaben, kuma zai bi duk wata hanya wajen kwato wannan nasara ciki har da zuwa kotu.

“Za mu bi duk wata hanya da doka ta tanada domin kwato hakkinmu. Mu ne muka lashe zaben, kuma za mu gabatarwa da ‘yan Najeriya da hujja." Obi ya ce yayin taron manema labaran da ya zamanto na farko tun bayan zaman.

A cewar Obi, zaben ya gaza hawa mizanin sahihanci, yana mai cewa, wannan zabe zai kasance mai cike da takaddama da Najeriya ta taba gudanarwa.

Shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce duk wanda yake da korafi da sakamakon zaben ya garzaya kotu.

XS
SM
MD
LG