Accessibility links

Muguwar Guguwa ta Yi Barna a Tsakiyar Yammacin Amurka


Gidan da ruwa ya yi gaba da shi

Ba'a gama kai doki kasar Philipines ba sai gashi muguwar guguwa ta ratsa tsakiyar yammacin Amurka

Wata muguwar guguwa da ambaliyar ruwa sun addabi tsakiyar yammacin Amurka jiya Lahadi inda akalla mutane biyar suka rasa rayukansu.

Duk mutanen da suka mutu daga jihar Illinois suke, jihar da muguwar guguwar ta fi shafa.

Guguwar ta kashe mutum daya a wani kauye mai suna Washington inda guguwar ta shafe duk anguwoyin. Tuni aka tura dakarun kare cikin gida dake jihar Illinois su goma domin ceto wadanda watakila suna da rai.

Wani dattijo da 'yaruwarsa lamarin ya ritsa dasu yayin da muguwar guguwar ta yi awon gaba da gidansu a garin New Minda dake kudancin jihar.

Muguwar guguwar mai tsananin gudu ta yi sanadiyar dakatar da zirga zirgan jirage a filayen sauka biyu O'Hare da Midway. Ta kuma yi sanadiyar dakatar da wasan kwallon kafa irin na Amurka tsakanin 'yan wasan Chicago da na Baltimore har na sa'o'i biyu .

Ban da haka muguwar guguwar ta shafi wasu jihohin dake makwaftaka da jihar Illinois kamar su Michigan da Indiana da Kentucky da Ohio inda ta bar dubun dubatan mutane da rashin wutar lantarki
XS
SM
MD
LG