Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaukaciyar guguwar teku "Haiyan" ta kashe akalla mutane 100 a Philippines


Jiya Juma'a, daya daga cikin mahaukaciyar guguwar teku mafi karfi da aka taba gani a kasar Phillippines, tayi barnar a kusan ko ina a kasar, harda kashe akalla mutane 100.

Jiya Juma'a, daya daga cikin mahaukaciyar guguwar teku mafi karfi da aka taba gani a kasar Phillippines, tayi barnar a kusan ko ina a kasar, harda kashe akalla mutane 100.
Yankunan kasar da dama suna cikin duhu, gashi kuma hanyoyin sadarwa sun lalace, a yayinda mahaukaciyar guguwar teku da aka lakawa suna Haiyan ta fada tsibiran Leyte da Samar.

Gidan talibijin na kasar ya nuna hoton vidiyon igiyar ruwa da ambaliyar ruwa da kuma kwararowar laka. An kwashe fiye da mutane dubu saba'in daga gidajensu a larduna ashirin da tara.

Hadarin da aka lakawa suna Yolanda tazo da iskar dake juyawar fiye da kilomita dari uku da hamsin cikin sa'a guda.

Jami'ai sun tabbatar da mutuwar mutane uku, bakwai kuma sunji rauni, kila kuma yawan wadanda suka mutu ya karu. A saboda katsewa ko kuma lalacewar hanyoyin sadarwa, ba'a tantance irin barnar da wannan mahaukaciyar guguwar teku ta yi ba.

Ana kyauta zaton, yau Asabar mahaukaciyar guguwar zata isa tekun kudancin kasar China, inda ake zaton zata kara karfi ta doshi kasar Vietnam.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG