Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhawara Kan Sallamar Shugabannin Rundunonin Tsaron Najeriya


Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Ranar Soja A Zamfara
Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Ranar Soja A Zamfara

A Najeriya ana ci gaba da tafka muhawara dangane da canza shugabannin rundunonin tsaro na kasar musamman duba da yadda matsalar tsaron kasar ke Kara daukar wani sabon salo.

Matsalar tabarbarewar tsaro itace babbar matsalar da ta fi ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya gabanin zuwan wannan gwamnati, abin kuma da ta yi kamfe dashi jama'a suka zabeta a shekarar 2015. Kuma jim Kadan da darewarta bisa karagar mulki ta tunkari matsalar ta Boko Haram gadan gadan, Inda har aka kwato dajin Sambisa dake zama tungar mayakan Boko Haram.

Yayin da ake jinjinawa gwamnatin bisa yadda ake ganin ta karya lagon Boko Haram, a daya bangaren kuma matsalolin tsaron cikin gida a Najeriyar sai ‘kara ta'zzara yake. Kama daga rikice-rikicen kabilanci, dauki ba dadi tsakanin manoma da makiyaya zuwa kashe-kashen ‘yan bindigar dake hallaka mutane ba gaira ba dalili a wasu jihohin dake Arewa maso yamma.

Ganin yadda matsalolin suka ki ci suka ki cinyewa hakan ya sa wasu yan Najeriya musamman ‘yan kungiyoyin fararen hula ke tababar cancantar sauke baki daya shugabannin rundunonin tsaron Kasar, hade da sufeta Janar na ‘yan sandan Najerya da Darakta Janar na hukumar ‘yan sandan ciki wato DSS.

Tsohon Babban kwamandan runduna ta bakwai ta sojojin Najeriya, Manjo Janar Junaid Bindawa mai Ritata na mai cewa shi bai ga wani aibi bisa daukar duk wani mataki da zai haifarwa sha'anin tsaro da mai Ido ba.

A nasa bangaren, masanin tsaro wing Kwamanda MUSA Isa salmanu cewa yake yi canza shugabannin rundunonin tsaron a Zahiri ba shine maslaha ba, amma sake fasalta tsarin tsaro shine kurum mafita. Domin matukar ba ai hakan ba to koda an canza Hafsoshin tsaron suma sabbin da za a nada din gaba kadan za a fara kiraye-kirayen suma din a canza su.

Batun canza shugabannin rundunonin tsaron kasar na ci gaba da raba kawunan masana tsaro a kasar, duk da dama wa'adin su tuni ya kare, amma Shugaba Muhammadu Buhari ya kara masu wa'adin shekara daya, wa'adin da shi dinma yanzu yake dab da karewa.

Yanzu dai abin jira a gani shine irin matakiin da Shugaba Muhammadu Buhari zai dauka yayin da wa'adin nasu ya kare nan da yan watanni kadan masu zuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG