Accessibility links

Ta’ Aziyyar Rasuwar Ojukwu A Ibadan

  • Hasan Tambuwal

Toshon madugun 'yan tawayen Biafra mai neman ballewa daga Nigeria Chukuemeka Ojukwu.

‘Yan Nigeria na ci gaba da yin ta’aziyya ga iyalai da ‘yanuwan Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, tsohon shugaban Biafra, wadda ta anemi ballewa daga tarayyar Nigeria, kuma tsohon shugaban jam’iyyar APGA a Nigeria.

Saurari:

Majiyar dake da nasaba da marigayi Ojukwu a birnin Ibadan jihar Oyon Nigeria ta tabbatar da cewa a daren Asabar ya rasu a wani Asibitin birnin London. A tattaunawar da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka abirnin Ibadan Hasan Umaru tambuwal yayi da mafi yawan al’ummar Igbo mazauna garin Ibadan sun yi addu’a tare da fatan za’a yi koyi da abubuwan da Ojukwun ya koyar kuma ya bari a baya. Mafi yawan al’ummar Igbo sun yada da halin zaman rayauwar marigayi Ojukwu, wanda suka abayanna da sunan babansu ne.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG