Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 78 Ne Suka Mutu a Fashewar Lebanon


'Yan kwana-kwana a Beirut na kashe wuta.
'Yan kwana-kwana a Beirut na kashe wuta.

An samu wata gagarumar fashewa a tsakiyar birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon da yammacin jiya Talata, lamarin da hallaka mutane sama da 78 kana wasu dubu hudu suka jikkata.

Fashewar ta faru ne a kusa da tashar jirgin ruwan birnin Beirut, lamarin da ya jijjiga birnin inda ya lalata gine-gine da motoci, babu abin da ake gani a kan tituna sai baraguzai.

Saboda karfin fashewar har a makwabciyar kasar Cyprus, mai tazarar daruruwan kilomita mutane sun ji motsinta, haka Kuma ta haddasa girgizar kasa mai karfin maki 3.3 a cikin babban birnin na Lebanon.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, fashewar ta kashe a kalla mutum 78, a cewar ministan kiwon lafiyar kasar Hamad Hassan. Shi ma kamfanin dillancin labaran Reuters, ya bada rahotan cewa a kalla mutum dubu hudu sun jikkata.

Hassan ya kara da cewa har ya zuwa wannan lokaci mutane da dama sun bata ba a san inda suke ba. Wasu kuma na zuwa sashen kulawar gaggawa domin neman 'yan uwa da abokan arziki.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahotan, ana samun bayanai masu cin karo da juna a kan abin da ya haddasa fashewar, wanda tun farko ake zaton wani wurin ajiyar kaya ne dake kusa da tashar jirgin ruwa dake cike da kayan wuta ya haddasa fashewar, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar na NNA.

Daga bisani, daraktan hukumar tsaron kasar ya ce wasu ababen fashewa ne da hukuma ta ajiyesu tsawon shekaru ne suka haddasa fashewar, amma kuma bai yi wani karin bayani ba.

Firai ministan Lebanon, Hassan Diab, ya sanar da fara gudanar da binciken musababbin fashewar.

Binciken zai hada da labarin da ya fito a kan sanarwar dakin ajiyar kayan dake dauke da abubuwan fashewa masu hadarin gaske tun cikin shekarar 2014, inji Firai Ministan, amma bai bayar da wani karin bayani ba.

Mallam Tijjani Hassan Daurawa, wani dan Najeriya ne mazaunin birnin na Beirut, ya shedi yadda lamarin ya faru inda ya yiwa Sashen Hausa na Muryar Amurka karin bayani a kan munin lamarin, Ga kuma tattaunawa da ya yi da Baba Yakubu Makeri:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG