Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunar Guguwa Ta Halaka Mutum 150 A Gabashin Afirka

Yadda guguwar ta mamaye wani yanki na kasar Zimbabwe, ranare 15 ga watan Maris, 2019.
Yadda guguwar ta mamaye wani yanki na kasar Zimbabwe, ranare 15 ga watan Maris, 2019.

Ita wannan mahaukaciyar guguwar ta sauka ne a ranar Alhamis a kusa da gabar garin Beira da ke Mozambique, tare da guguwa mai tafiyar kusan kilo mita 200 sa’a guda.

Sama da mutane 150 sun rasa rayukansu sannan wasu daruruwan sun bata a jiya Lahadi bayan da wata mahaukaciyar guguwa da aka wa lakabi da Idai ta ratsa ta kudu maso gabashin Afrika.

Majalisar Dinkin Duniya ta ba da kiyasin da ya nuna cewa mutum miliyan daya da rabi ta mummunar guguwar ta shafa a Mozambique, Malawi da kuma Zimbabwe.

Sannan dubun dubatar mutane suka rasa hanya da kuma wayar sadarwa a mafi yankunan karkara inda talakawa ke zaune.

Ita wannan mahaukaciyar guguwar ta sauka ne a ranar Alhamis a kusa da gabar garin Beira da ke Mozambique, tare da guguwa mai tafiyar kusan kilo mita 200 sa’a guda.

Daga nan ne kuma guguwar ta nausa yamma zuwa Malawi da kuma Zimbabwe.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane 122 su ka mutu a Mozambique da Malawi.

Sannan a jiya Lahadi, Jami’ai a Zimbabwe sun tabbatar da mutuwar mutum 65.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG