Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunar Guguwar Teku Ta Tinkaro Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, fadar White House a shirye take tsaf, yayin da guguwar teku take kadowa ta dira a gabar tekun gabashin kasar.

Guguwar tekun da aka ba lakabi Florence tana da hatsarin gaske da karfin maki hudu wadda take gudun kimanin kilomita dari biyu da ishirin cikin sa’a guda.

Masu harsashe sunce suna kyautata zaton guguwar ruwan zata kasance da karfi a lokacin da zata isa jihohin Carolina ranar alhamis ko jumma’a da safe.

Akwai yiwuwa guguwar ta Florence ta karkata ta nufi jihohin Virginia da Maryland da Delaware da kuma gudummuwar Kwalambiya dake kan hanyarta.

Jiya Talata shugaba Trump ya sa hannu a takardar da ta ayyana jihohin Carolina da Virginia a matsayin inda ake da bukatar gaggawa. Abinda zai bada damar bada agajin gwamnatin tarayya. Ya kuma shawarci wadanda ke zaune a wadannan jihohin su fice domin lamarin zai yi munin gaske.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG