Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Daji Ta Tilasta Rufe Wata Babbar Hanya a Jihar California


Wutar Daji a California

A jihar California wutar daji ta tilasta rufe wata babbar hanya data rasta illahirin yammacin Amurka har zuwa jiya Lahadi sakamakon wutar d a take ci babu kakkautawa a arewacin jihar.

Wutar da tuni ta kona kadada dubu 16 da 600, ta tilasta rufe hanyar da ake kira Interstate 5, na tsawon kilomita 72, babbar hanya ce a ake zirga zirga kasuwanci mai yawan gaske, kwanaki biyar kenan wutar tana ci.

Wutar ta tilastawa matuka manyan motoci su arce su bar motocin nasu. Jami'ai suka ce akalla manyan motoci 17 ne matuka suka gudu suka bar su, a cikin su 5 tuni wuta ta kone su.

Jami'an 'yan kwana-kwana suka ce tun ranar laraba wuta r ta tashi, sun hakikance take taken mutane ne suka haddasa ta, sai dai basu san ko dagangan aka cunnata ba.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG