Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Da Burin Mu Yi Aiki Tare Da Sabuwar Shugabar Tanzania - Buhari


Buhari, hagu, sabuwar shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, dama (Hoto: Instagram)
Buhari, hagu, sabuwar shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, dama (Hoto: Instagram)

Samia Suluhu Hassan, ita ce mace ta farko da ta zama shugabar kasa a Tanzania mai yawan jama’a sama da miliyan 58.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari​ ya mika sakon taya murna da fatan alheri ga sabuwar shugabar kasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan wacce ta maye gurbin marigayi John Magufuli wanda ya rasu a ranar Laraba.

Samia ita ce mataimakiyar Magufuli wanda rasu yana da shekara 61 bayan fama da matsalar bugun zuciya a cewar hukumomin kasar.

Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari​, Samia Suluhu Hassan, John Magufuli, da Tanzania.

“Shugaba Muhammadu Buhari, na taya mataimakiyar shugaban kasa Samia Suhulu Hassan yayin da ta karbi ragamar mulkin kasar bayan mutuwar shugaba John Magufuli.” Kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Samia ita ce mace ta farko da ta taba zama shugabar kasa a Tanzania mai yawan jama’a sama da miliyan 58.

Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga Samia da ta yi amfani da wannan dama wajen hada kan ‘yan kasar tare “da dora ta bisa turba madaidaiciya.”

Sanarwar ta Garba Shehu, ta kuma nuna cewa shugaba Buhari a shirye yake ya yi aiki da sabuwar shugabar wajen tunkarar batutuwan da suka shafi Afirka da duniya baki daya.

Wannan Zai Zaburar Da Mata Wajen Neman Mukami - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar shi ma ya bi sahun masu taya Samia murnar zama shugabar kasar ta Tanzania.

A wani sako da ya wallafa a shafin Twitter, Atiku wanda tsohon dan takarar shugaban kasa ne karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ya yi fatan wannan matsayi da Samia ta kai zai kwadaitar da sauran matan Afirka wajen kai wa ga wannan mukami.

“Fatana shi ne, wannan daukaka da ki ka samu, za ta kwadaitar da sauran matan Afirka su ji kiran da ake musu na su fito su yi wa gwamnati hidima.” Atiku ya ce.

A ranar Laraba mataimakiyar shugaban kasa Samia Suluhu ta sanar da mutuwar shugaba Magufuli, wanda ta ce ya yi fama da cutar bugun zuciya.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ce a ranar Laraba mataimakiyar shugaban kasa Samia Suluhu ta sanar da mutuwar shugaba Magufuli, wanda ta ce ya yi fama da cutar bugun zuciya.

Rabon da a ga John Magufuli a baina jama’a, tun a watan Fabrairu kuma manyan jami’an gwamnatinsa sun musanta raderadin da ake yi cewa ba shi da lafiya, duk da cewa ana ta yadawa a kafafen sada zumunta cewa mai yiwuwa har ya fita a hayyacinsa sanadiyyar rashin lafiyar.

Marigayin na daya daga cikin fitattun mutane a nahiyar Afirka da ke nuna shakku kan cutar COVID-19.

A bara, ya fito ya bayyana cewa kasar ta Tanzania ta kawar da cutar baki daya bayan kwana uku da aka kwashe ana addu’o’i a kasar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG