Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Gaggauta Kawar da Kungiyar Boko Haram-Shugaba Buhari


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya ya sake jaddada aniyar gwamnatins na kawar da kungiyar Boko Haram cikin dan lokaci

Yau a Abuja shugaba Buhari ya sake nanata aniyarsa da ta gwamnatinsa na ganin an kawar da kungiyar Boko Haram cikin dan gajeren lokaci.

Idan aka yi la'akari da yadda Najeriya da kawayenta ke yaki da kungiyar za'a san cewa nan ba da dadewa ba za'a kawo karshen 'yan ta'adan.

Yayinda yake magana da Mr Mousa Faki Mahamat ministan harkokin wajen kasar Chadi kuma jakadan Shugab Idris Deby na musamman shugaba Buhari yace irin karfin gwiwar da sojoji suke dashi yanzu tare da samun ingantacen horo da makamai na kwarai karshen 'yan ta'ada da ta'adanci ya doso.

To saidai shugaban ya kara kiran Najeriya da Chadi su kara sadakar da kai domin gaggauta kawo karshen wannan muguwar kungiya ta Boko Haram. Yace nan ba da dadewa ba zamu murkusheta.

Kullum ana raunata kungiyar kuma idan aka cigaba da hakan za'a ga karshenta da duk mayakanta.

XS
SM
MD
LG