Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Goyon Bayan Zaben Kashim Shetima A Matsayin Mataimakin Tinubu-Gwamnonin APC


Buhari, Tinubu da Shettima.
Buhari, Tinubu da Shettima.

Kungiyar gwamnonin APC ta mara baya ga zaban Kashim Shettima a matsayin mataimakin Bola Tinubu a takarar zaben 2023.

Shugaban kungiyar gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya zayyana haka a lokacin da ya gana da shugaba Buhari a Daura.

Wannan dai na nuna gwamnonin sun mika wuya ga zaben Shetima maimakon daukar daya daga cikin su ya zama mataimakin.

Tun farko an yayata cewa gwamnan Kaduna Nasiru Elrufai da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na daga cikin wadanda a ke sa ran ba wa mukamin.

Bagudu ya ce farar dabara ce daukar wanda bai gaza matsayin Shettima ba kan mukamin takarar.

Hakanan shi ma gwamnan jihar Borno Umara Zulum ya nuna farin ciki da cankar Shetima a mataimakin, duk shi ma an yi ta yayata sunan sa don daukar sa a mukamin.

Zulum ya zayyana wannan abun tamkar shi a ka yi wa don Kashim maigidansa ne.

Atiku Bagudu wanda ya ke tare da wasu daga gwamnonin APC a ziyarar, ya ce ba mai adawa da matsayar da a ka dauka.

Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dr.Abubakar Umar Kari ya ce duk jam’iyyun na da kalubale amma ba za a iya cewa kai tsaye ‘yan adawa za su iya kada gwamnati ba ko kuma a ce kai tsaye APC za ta zarce.

Masu azancin zance na cewa inda ba kasa a ke gardamar kokawa, amma gaskiya abun da ya zama zahiri shi ne ba karkashi a jikin jama’a kan babban zaben in an kwatanta da na 2011 da 2015 da a ke batun ko Buhari ko rijiya. Ba don ma zaben ya zama dole a yi ba, wasu sun dawo daga rakiyar cika bakin ‘yan siyasa.

Saurari cikaken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

XS
SM
MD
LG