Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekaru 75 Da Kafuwa: Muryar Amurka Ta Yi Nazari Kan Makomar Aikin Jarida A Jami'ar George Washington

Muryar Amurka da Jami’ar George Washington sun gudanar da wani zaman tattaunawa akan makoma da kuma halin da aikin jarida yake ciki yanzu a duniya.

Tattaunawar dai wani bangare ne na ci gaban shagulgullan da ake na cikar shekaru 75 da kafa gidan rediyon Muryar Amurka na VOA. Dalibbai da dama na jami’ar ta GWU suka halarci zaman domin fahimtar muhimmancin aikin jarida daga kwararu da suka hada da tsohon shugaban Muryar Amurka kuma darekta aikin jarida da tsaron kasa na jami’ar, David Ensor da Alhaji Aliyu Mustapha Sokoto, Babban Edita na Sashen Hausa da kuma Euna Lee mai tsara shirye shiryen Telbijin ta sashen Korea. An dai yi zaman ne ran 2 ga watan Afrilu na shekarar 2018.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG