Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi Da Kirista Na Kokarin Kara Zama Tsintsiya Madaurinki Daya Don Samar Da Kwanciyar Hankali A Kasar.


Taron shugabannin addinai

A Najeriya  lokuta masu daraja ga manyan addinai biyu na kasar  na karkata tunanin jama'a ga kyautata cudanya tsakanin juna don nema wa kasar zaman lafiya mai dorewa.

Wannan na zuwa ne lokacin da Musulmi da kirista ke kokarin kara zama tsintsiya madaurinki daya don nemar wa kasa zaman lumana.

Lokacin Ista da na Ramadan lokuta ne biyu masu daraja ga mabiya addinin Kirista da na Musulunci a duniya baki daya, kuma lokuta ne da mabiya addinan kan kara azama wajen neman kusanta ga ubangiji.

A Najeriya wasu lokuta idan ana gudanar da ibada ta addini akan samu mabiya wani addini suna taya takwarorinsu murna ko wata hidima ta addini, kamar yadda ya sha faruwa tsakanin Kirista da Musulmi.

Wannan karon da aka samu lokacin Ista ya fado cikin Ramadan sai ya kara karfafa gwiwar cudanyar mabiya addinan biyu kamar yadda suka hadu wurin buda baki na azumin da Musulmi ke yi a Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan cudanyar, tun dayake ba yanzu aka fara ta ba tsakanin mabiya addinan, wane tasiri za a ce an soma gani wanda kan sa a samu biyan bukatar haduwar? Tuni aka soma bayyana alfanun hakan.

Duba da yanayin da Najeriya ta samu kanta ciki a halin yanzu ya kara karkata tunanin mabiya addinan akan cewa irin wannan haduwa za ta taimaka ga warware masu matsalolin da ke addabar jama'a, kamar yadda shugaban kungiyar baki mazauna Sakkwato, Ishaya Bagai yake gani.

Wannan haduwar na faruwa lokacin da ake ta samun rahotannin kai hare-hare ga wasu al'ummomi a Jihohin Sakkwato da Kebbi da ma wasu Jihohin arewacin Najeriya, inda ‘yan bindiga ke kisa tare da satar mutane don neman kudin fansa duk da yake mahukumta na cewa suna kan kokarin shawo kan matsalolin.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG