Accessibility links

Musulmi Masu Aikin Haji Sun Yi Jifan Shedan


Musulmi masu aikin Haji na jifan shedan.

Dubban daruruwan Musulmi sun yi jifan shedan a yau Lahadi bayan sun yi hawan Arfa a jiya Asabar

Jami’an gwamnatin kasar Saudiyya sun ce Musulmi fiye da miliyan biyu da rabi ne su ka yi Hajin bana. Haji ne aikin Ibada mafi dadewa a duniya kuma mafi tsarkaka a addinin Islama, kuma ya wajabta akan dukkanin Musulmi maza da mata masu hali da kwarin jiki. A Makka aka haifi Annabi Muhammad (SAW).

Dubban daruruwan Musulmi sun yi jifan shedan a yau Lahadi bayan sun yi hawan Arfa a jiya Asabar. Wajibi ne ga kowane alhaji ya jefa duwatsu 21,wato dutse 7-7 a kan kowace jamra daya daga cikin ukkun dake jere a zaman shedan.

Wani alhaji ya tattakura zai jefi shedan
Wani alhaji ya tattakura zai jefi shedan

Bayan jifan shedan sai alhazai su koma Makka su yi dawafi a Dakin Kaaba, wanda a jikin shi dutsen shan nono (Hajr Aswad) ya ke makale, shima dutsen yana daga cikin abubuwan tarihin Addinin Islama mafiya tsarkaka.

Haka kuma a yau Lahadi ake Eid al-Adha wato Sallar Layya, ta yankan sadaka domin tunawa da lokacin da Annabi Ibrahim (AS) Ya bi umarnin Allah (SWT) Ya kusa yanka dan shi Annabi Ismail (AS).

XS
SM
MD
LG