Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Amurka Tace Rasha Zata Iya Sake Yin Katsalanda A Zabukan Amurka


Sojojin Amurka
Sojojin Amurka

Sauran kwanaki kalilan a yi zaben rabin wa’adi a Amurka kuma a wannan lokaci ana kara samun fargabar cewa Rasha zata iya sake yin katsalandan a harkar demokaradiyar Amurka daga yanzu har izuwa zaben shugaban kasa a shekarar 2020.

Jami’an tsaro da na soji sun nuna damuwa game da aniyar Moscow na haddasa rikici da rarraba tsakanin Amurkawa domin ta ga tayi nasara a kan sojan Amurka, wannan karo bada harsashi ba ko kuma muggan makamai amma ta hanyar aikewa da sakonnin Twitter da yada sakwanni ta yanar gizo

A ciki dabarun Rasha, tana kokarin neman inda akwai rikici ko rarraba tsakanin jama’a a Amurka domin ta kara dagula al’amura ta hanyar fadada baza sakwannin raba kan al’ummar.

Game da sojan Amurka, jami’an sojan na yanzu da na da, sun ce akwai yiwuwar manufar Kremlin ce ta samu tasiri a kan sojojin Amurka, ta hanyar aikewa da bayanan karya ga sojojin Amurkan kuma Rasha zata iya sa sojojin sun yanke shawarwarin da ita take so.

Sai dai ba a iya gano matsayin yanda Rasha ta auna jami’an sojan Amurka ba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG