Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 20 Sun Mutu A Zanga-zangar Kin Jinin Shugaban Dimokradiyar Congo


Wani cikin masu zanga zanga ya fadi bayan da 'yansanda suka budewa mutane wuta
Wani cikin masu zanga zanga ya fadi bayan da 'yansanda suka budewa mutane wuta

Kin barin mulki bayan wa'adinsa ya kare da Joseph Kabila yayi a kasar Congo ya soma haddasa rikici tare da salwantar rayuka a babban birnin kasar

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya ko MDD sun bada rahoton cewar mutane 20 sun mutu a birnin Kinshasa na kasar Congo-Kinshasha bayan wani rikici da ya barke a lokacin wata zanga zangar kin jinin shugaban kasar Joseph Kabila wanda wa’adin mulkinsa ya kare shekaranjiya Litinin amma ya ki ya sauka daga mulki, bayan ya kwashe shekaru da dama yana mulkin kasar.

Sashen Faransanci na Afrika na Muryar Amurka ya tabbatar da mutuwar mutane uku daga cikin wadanda abin ya shafa.

Mazauna wasu unguwanni a cikin babban birnin Congo sun yi ta bushe bushe da tsakar dare don sun janyo hankalin shugaba Kabila da cewar wa’adinsa ya cika don haka ya sauka daga mulki.

An ci gaba da jin karar harbe harben bindiga a wasu larduna har zuwa jiya Talata.

A ranar Litini, masu zanga zangar sun mamaye unguwanni da dama a cikin birnin Kinshasa duk da haramci da aka dorawa yin zanga zangar da kuma yawan sojoji a cikin birnin. Shedu sun ce yan sanda sun watsa barkokno tsohuwa don tarwatsa masu zanga zangar.

XS
SM
MD
LG