Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 7 Aka Kashe A Garin Gashuwa


Gawarwakin mutanen da suka mutu a Damaturu a cikin jerin hare-haren baya-bayan nan da aka shirya kaiwa a lokaci daya

Harbe-harbe ya barke a garin Gashuwa dake Jihar Yobe a arewacin Najeriya, tsakanin ‘yan bindiga da jami’an tsaro inda mutane 7 suka mutu.

A daren jiya Laraba ne tsakanin karfe 12 zuwa karfe 1 na dare, fada ya barke tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga, inda jami’an tsaro suka rasa ‘yan sanda guda biyu, sannan suka kashe ‘yan bindiga su 5.

Sai dai sun yi nasarar kama mutum 3 da suke zargi na da alaqa da harin.

Mutane a wannan gari dake misalin kilomita 185 daga babban birnin Jihar, Damaturu, sun share wunin yau Alhamis baki daya a cikin gidajensu, ba tare da zuwa kasuwa ba ko wuraren ayyukansu.

Mazauna Gashuwa na jiran Gwamnati ta basu izinin fita waje, kuma dama garin na karkashin dokar hana fita waje daga karfe 6 na yamma zuwa wayewar gari.

Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda ya tattauna da wani mai fada da yawun rundunar JTF a Jihar ta Yobe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG