Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 8 Sun Mutu Sakamakon Rugujewar Wani Bene a Birnin Legas


Ma'aikatan agaji suna neman masu rai a ginin Cocin daya rushe mallakan Cocin Synagogue, a Lagos, 16 ga Satumba, 2014.
Ma'aikatan agaji suna neman masu rai a ginin Cocin daya rushe mallakan Cocin Synagogue, a Lagos, 16 ga Satumba, 2014.

Wani bene mai hawa uku, wanda iyalai ke ciki, ya rushe a babban birnin hada hadar kasuwancin Najeriya na Legas, inda mutane 8 suka mutu wasu su 23 kuma suka jikkata, wadanda aka kai su asibiti, a cewar hukumar kai daukin gaggawa a yau Litinin.

Faduwar gine gine dai ba bakon abu ba ne a wannan kasa mafi yawan al’umma a Afirka, inda miliyoyin mutane ke zama cikin gidaje marasa inganci, kuma akasarin lokuta ake watsi da ka’idodin gina gidaje.

Benen mai hawa 3 ya ruguje ne da daren jiya Lahadi, a unguwar Ebute-Metta, da ke wannan birni mai yawan al’umma sama da miliyan 20, abinda Ibrahim Farinloye na hukumar Kai Daukin Gaggawa ta NEMA ya fada wa kafar labaran AFP kenan.

“Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 9:30 na dare. Gini ne mai hawa uku. An yi amfani da ginin kasa da bene na daya a matsayin wurin ajiye kayayyaki yayin da hawa na biyu da na uku jama’a ke zama a ciki,” a cewarsa.

Farinloye ya ce ana ci gaba da aikin ceto a wurin da lamarin ya faru. Ya kuma ce ana gudanar da bincike domin gano musabbabin rugujewar ginin na baya bayan nan a kasar.

A watan Janairu, mutane uku, ciki har da yara biyu, suka mutu aka kuma kubutar da wasu 18, a lokacin da wata majami’a ta ruguje a jihar Delta da ke kudancin kasar.

Batun bin ka’idojin gine-gine ya fara daukar hankali tun bayan da wani katafaren bene da ake ginawa ya ruguje a Legas a watan Nuwamban bara, inda mutane akalla 45 suka mutu.

Tun daga shekarar 2005, akalla gine gine 152 ne suka ruguje a Lagas, a cewar wani mai bincike na jami’ar Afirka ta Kudu.

XS
SM
MD
LG