Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Gini Mai Hawa Sama Da 20 Ya Rufta Akan Ma'aikata A Legas

Wani bangaren ginin da ya rushe a Legas
Wani bangaren ginin da ya rushe a Legas

Ruftawar gine-gine a jihar  Legas da ke kusa da teku, abu ne da ya sha faruwa inda a lokuta da dama akan dora alhakin hakan akan masu gine-gine da ke amfani da kayan gini marasa inganci.

Rahotanni daga Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya na cewa wani gini mai hawa 21 da ake kan ginawa ya rushe, ana kuma fargabar ya danne mutane da dama.

Lamarin ya faru ne a yankin Ikoyi a ranar Litinin, hukumomin kuma na kokarin ceto wadanda ginin ya rufta a kansu wadanda ba a san adadinsu ba.

Bayanai sun yi nuni da cewa, jami’an kashe gobara da na hukumar ba da agajin gaggawa na hukumar NEMA na daga cikin wadanda suka hallar a wajen da ginin ya rufta da taimakawa.

Ruftawar gine-gine a jihar Legas da ke kusa da teku, abu ne da ya sha faruwa inda a lokuta da dama akan dora alhakin hakan akan masu gine-gine da ke amfani da kayan gini marasa inganci.

XS
SM
MD
LG