Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Ashirin Da Biyar Sun Mutu a wani Hadarin Mota a Nijer


Hadarin Mota

Gwamnan jihar Doso a Jamhuriyar Nijer Mallam Musa Usman, ya gargadi direbobi masu izinin tuki da su kiyaye ka’idojin tuki kuma su daina garaje a kan hanya.

Yace abu ne da aka sani duk matuki sai yasan sharudda amfani da hanya kamin a bashi izini, kafin direba ya fara tuki sai an bashi takardan izini kuma wannan izini na da sharudodin dake tattare dashi da yakamata a kiyaye.

Kalaman na gwanman Doso Musa Usman ya biyo bayan wani mummunar hadarin mota da ta auku a jihar ta Doso da ya hallaka rayuka ashirin da biyar nan take kana mutum guda ya mutu yayin da aka isa dashi a asibiti. Mutane ashirin da hudu ne suka jikata, takwas a cikinsu kuma na cikin matsanancin hali.

Wannan kazamin hadarin da ya hada wata babban motar sufuri ta wani kanfanin STM da motocin hayis guda biyu da ya auku kimanin kilomita uku daga Doso, yasa yan sandan sun gaggauta kai dauki a wurin. Yan sanda sun ce suna ci gaba da binciken makasudin wannan hadarin.

Mallam Muntari Dumbiya shine shugaban yan sandan jihar Doso, ya shaidawa wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka cewar labarin da suka tattara da fari shine babban motar bos ne yake kokarin wuce kananan motocin abin da ya haifar da cin karo da motocin na gaba.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG