Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Goma Sun Mutu A Girgizar Kasa a Indonesia


Wata girgizar kasa mai karfi maki 6.4 ta ratsa tsibirin Lambok na kasar Indonesia kuma ta kashe akalla mutane goma kana wasu arba'in suka jikata.

Wannan girgizar kasar mai zurfin kilomita bakwai daga kasa, ta bugi shahararren gandun yawon shakatawa ne da safiyar yau Lahadi, lamarin da ya kora mutane zuwa kan ticuna da sararin da babu gien gine don kada su rushe a kansu.

Mai Magana da yawun hukumar kawar da bala’i ta Indonesia yace alkalummar da suke ci gaba da tattarawa, akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu zai karu.

An ji kuma girgizar kasar a tsibirin Bali dake makwabtaka da inda abin ya faru.

Girgizar kasar wata aba ce da aka saba gani a Indonesia saboda kasancewarta dab da tekun Pacific, yanki mai tattare da girgizar kasa da kuma aman wuta daga tsaunuka.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG