Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Na Kaucewa Gwajin Coronavirus A Amurka


Amurkawa
Amurkawa

Adadin gwajin tabbatar da cutar coronavirus a Amurka a duk rana ta Allah yayi kasa a karon farko, duk da kira sashen kiwon lafiyar jama’a da jami’an tarayya ke yi da a kara yawan gwaje gwaje a Amurka.

Amurka dai itace kan gaba wurin yawan mutanen da suka kamu da cutar da wadanda suka mutu da cutar a duniya.

Alkalumma daga tsarin bibiyar COVID, wanda ke daukar kan sa a matsayin “aikin hadin gwiwa da ma’aikatan sa kai ke gudanarwa” domin bibiyar barkewar cutar a cikin kasar, sun yi nuni da gwaje gwajen ya yi kasa ainun fiye da makwanni biyu da suka shude.

Kididdiga daga aikin bibiyar cutar, wanda fadar White House da wasu hukumomi ke yawan amfani da ita wurin tattara bayanai, ta nuna ana gwajin mutum dubu 733 a Amurka a kowace rana a cikin watan Agusta, adadin ya dan yi kasa a kan mutum dubu 750 da ake musu gwaji a watannin baya. Kayyadadden adadi na cikin kowane wuni a mako, ya sauko zuwa dubu 709 a ranar Litinin kafin zuwa karshen mako ya kuma haura.

Fadiwar adadin da ya faru bayan watanni da dama da ake yawan gwaji, za a iya alkanta shi karancin mutane dake zuwa gwajin cutar biyo bayan sake kunno kai da cutar ta yi a wannan lokacin rani lamarin da yasa mutane ke kaucewa yin gwaji saboda daukar lokaci wurin jiran sakamako da kuma jinkirin fitowar sakamakon.

Ya zuwa jiya Asabar, mutane da suka kamu da COVID-19 a fadin duniya sun kai sama da miliyan 21 a cewar jami’an John Hopkins. Sama da mutum miliyan biyar da dubu dari uku ne suka kamu da cutar a Amurka, kana Brazil na biye da ita da mutum miliyan uku da dubu dari biyu da suka kamu da coronavirus.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG