Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Sun Rage Mutuwa Ta Dalilin Zazzabin Cizon Sauro


Wata ma'aikaciyar dakin binciken kwakwa

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, ana ci gaba da samun raguwar mutuwar al’umma ta dalilin kamuwa da zazzabin cizon sauro tun daga shekara ta dubu biyu, watau shekaru goma sha uku yanzu

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, ana ci gaba da samun raguwar mutuwar al’umma ta dalilin kamuwa da zazzabin cizon sauro tun daga shekara ta dubu biyu, watau shekaru goma sha uku yanzu.

Darektan kula da ayyukan yaki da zazzabin cizon sauro na hukumar Dr. Fatoumata Nafo-Traore ce ta bayyana haka a wajen taron kolin shugabannin kasashen nahiyar Afrika kan yaki da cutar kanjamau da zazzabin cizon sauro da kuma tarin fuka da aka yi a babban birnin tarayya Abuja.

Dr. Nafo-Traore ta bayyana cewa, an ceci kimanin rayukan mutane sama da miliyan daya tun daga shekara ta dubu biyu yawancinsu kananan yara da shekarunsu basu kai biyar ba da suke zaune a nahiyar Afrika. Ta kuma ce an sami raguwar kamuwa da zazzabin cizon sauro a kasashe 44 na nahiyar Afrika.

Darektar ta kuma ce, dukan cibiyoyin dake talafawa a yaki da zazzabin cizon sauro zasu ci gaba da taimakawa domin ganin an sami nasarar shirin a kasashen Afrika. Ta bayyana cewa, duk da yake akwai kasashen da har yanzu ake samun masu fama zazzabin cizon sauro, amma babu kamar kasashen nahiyar Afrika. Ta kuma ce kasahen ne zasu jagoranci yunkurin kawar da cutar a duniya baki daya.

Bisa ga cewarta, ci gaba da aka samu a yaki da zazzabin cizon sauro a nahiyar Afrika alama ce cewa, za a sami nasarar cimma muradun karni a fannin inganta lafiyar mata masu ciki da kannan yara a kuma kawar da talauci. Tace ana samun ribar dala hudu a kan kowacce dala daya da aka kashe a yaki da zazzabin cizon sauro.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG