Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Takwas Ne Suka Rasa Rayukansu Bayan Tashin Bom A Maiduguri


Wata fashewar da ta auku a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ta Arewa maso Gabashin Najeriya, ta hallaka mutane akalla 8 a cewar hukumomi jiya Laraba.

Bom din ya tashi ne a wata motar taxi dake cike makil da mutane. Wannan shine fashewar bam mafi muni a wannan jiha mafi girma a Arewa maso Gabashin Nigeria bayan wasu watanni, acewar hukumomin.

Hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA, tace mutane 15 ne suka jikkata kuma ana kula da su yanzu haka a wani asibiti a yankin.

A wata sanarwa da hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta fitar, na cewar an kara karfafa matakan tsaro a inda bom din ya tashi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kafe a kan shafinsa na Twitter, inda yake bayyana alhininsa ga tashin bom a Maiduguri, kuma ya mika ta’aziyarsa ga iyalan wadanda tashin bom din ya rusa dasu da kuma gwamnatin jihar Borno.

XS
SM
MD
LG