Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Sudan Sun Kara Kaimi Wurin Matsawa Sojojin Kasar Lamba


Firai ministan Habasha, Abiy Ahmed da shugaban gwamnatin Sojin Sudan, General Abdel-Fattah Burhan
Firai ministan Habasha, Abiy Ahmed da shugaban gwamnatin Sojin Sudan, General Abdel-Fattah Burhan

Shugabannin masu zanga zanga a Sudan suna kira ga mutanen kasar su kara kaimi a ayyukan kalubalantar gwamnatin sojan kasar, biyo bayan amfani da karfin tuwo da sojojin suka yi a kan mutane a lokacin wani zaman dirshe.

Kungiyar masana a kasar Sudan ta SPA atakaice, wacce ke jagorantar zanga zangar da suka iza sojojin suka kifar da gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir, ta fada a jiya Asabar, cewa yau Lahadi ne zata bayyana matukar adawarta kuma zasu ci gaba da yin haka har sai sojojin sun mika mulki ga farara hula.

Kiran da shugabannin masu zanga zangar suke yi, na zuwa ne mako daya bayan da rundunar tsaro suka fara daukar matakan hana masu zanga zangar yin sansani a wajen helkwatan sojojin dake birnin Khartoum. Adadin mutanen da aka kashe daga ranar Litinin ya kai 113.

Kunagiyar masana a Sudan ta SPA, tace ta amince da Firai ministan Habasha a matsayin mai shiga tsakani kuma ya fara tattaunawa da gwamantin sojin kasar, koda yake kungiyar masanan ta bukaci a kafa wani bincike mai zaman kansa ya duba batun tashin hankalin da ya barke tun bayan kawar da shugaba al-Bashir

Firai ministan Habasha Abiy Ahmed, ya yi kira ga samun kwarin gwiwa yayin da ya gana da manyan sojojin masu mulkin kasar Sudan da shugabannin ‘yan adawa, a wani yunkurin kawo karshen rikicin siyasa da Sudan ta fada a cikin tun bayan hambarar da dadadden shugaban kasar Omar al-Bashir.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG